1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar raba mukamai a Sudan ta Kudu

Abdoulaye Mamane Amadou
June 17, 2020

Bangarorin da basa ga maciji a Sudan ta Kudu sun aminta da rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa domin kawo karshen yakin basasar da ya daidaita kasar.

https://p.dw.com/p/3dwlD
Südsudan Salva Kiir und Riek Machar | Entscheidigung für  Einheitsregierung
Hoto: AFP/A. McBride

Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar na Sudan ta Kudu, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a wannan larabar a karkashin jagorancin wasu kasashen waje da dama.

Bayan shafe tsawon lokaci suna kai ruwa rana, bangarorin biyu daga karshe sun cimma matsayar kafa wata gwamnatin hadin kan kasar tare da raba mukamai, a wani yunkuri na kawo karshen yakin basasar da ya yi sanadiyar hallaka dubban mutane a kasar.

Tuni dai bangarori da dama suka nuna gamsuwa kan wannan matakin da bangarorin biyu suka cimma, wanda tun a shekarar 2018 ta ke fuskantar tarnaki.