1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta kama masu leƙen asiri

Usman ShehuApril 29, 2012

Mahukuntan Khartum sun sanar da kama Turawa 'yan laƙen asiri a kan iyakarsu da Sudan ta Kudu

https://p.dw.com/p/14mlP
Sudanese President Omar Hassan al-Bashir waves to supporters after receiving victory greetings at the Defence Ministry, in Khartoum April 20, 2012. South Sudan said on Friday it would withdraw its troops from the disputed Heglig oil region more than a week after seizing it from Sudan, pulling the countries back from the brink of a full-blown war. Sudan quickly declared victory, saying its armed forces had "liberated" the area by force as thousands of people poured onto the streets of Khartoum cheering, dancing, honking car horns and waving flags. REUTERS/ Mohamed Nureldin Abdallah (SUDAN - Tags: MILITARY CONFLICT POLITICS) Generalleutnant Umar Hasan Ahmad al-Baschir (arabisch ‏عمر حسن أحمد البشير‎, DMG ʿUmar Ḥasan Aḥmad al-Bašīr; * 1. Januar 1944 in Hosh Bannaga bei Schandi, Sudan) ist der Staatspräsident des Sudan, der 1989 nach einem unblutigen Militärputsch an die Macht kam und das Land nach einer islamisch-fundamentalistischen Haltung regiert. Seit 1993 ist al-Baschir Staatspräsident.
Umar Hassan Ahmad al-Bashir, shugaban kasar SudanHoto: Reuters

Gwamnatin Sudan tace ta kama wasu yan leƙen asiri a inda suka taƙadda, kan iyakar ta da Sudan ta kudu. Kakakin sojojin Sudan Al-Sawarmi Khalid, yace baƙin da aka kama suna leƙen asiri, akwai yan ƙasar Birtaniya da Norway da Afirkas ta kudu, hade da yan Sudan ta kudu masu yi musu rakiya. Kakakin sojojin yace an tsare mutanen a yankin Heglig mai arzikin mai, inda suke taƙaddama da juba. A wani labarin kuwa gwamnatin Sudan ta kafa dokar ta baci a kan iyakar ta da Sudan ta kudu, abinda ya kara kawo matsin labba ga mahukunta Juba. Karkashin kudurin da Albashir ya zartas, an hana sayarwa al'ummar Sudan ta kudu kaya daga Sudan ta Arewa jihohin Kordofan, White Nile da kuma jihar Sennar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala