1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta hana Amurka aika soji don gadin ofishin jakadancita

September 15, 2012

Hukumomin Sudan sun ce ko kusa ba za su lamuncewa Amurka ta shigar da dakarunta ƙasar ba domin gadin ofishin jakadancin ta.

https://p.dw.com/p/169nE
Sudanese demonstrators attack the U.S. embassy in Khartoum September 14, 2012. Three people were killed on Friday during a demonstration against an anti-Islam film outside the U.S. embassy in Sudan, Sudan's state radio said. REUTERS/Stringer(SUDAN - Tags: POLITICS CIVIL UNREST RELIGION)
Sudan Khartum Angriff auf amerikanische BotschaftHoto: Reuters

Ministan harkokin wajen ƙasar ta Sudan Ali Ahmed Karti ne ya ambata hakan a wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran ƙasar SUNA inda ya ce Khartoum na da ƙarfin da za ta iya kare ofisoshin jakadancin ƙssashen duniya da ke ƙasar ba tare da an aike mata wasu mutane ba.

A jiya Juma'a ce dai wani jami'in gwamnatin Amurka ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewar Washington za ta aike da sojinta domin ƙarfafa tsaro a ofishin jakadanci bayan da masu zanga-zanga su ka afka masa biyo bayan nuna wani fim da aka yi a Amurka wanda ya yi kare tsaye ga Annabin tsira (SAW) da ma dai addinin Isalama baki ɗaya.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman