1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Sudan ta yi bankwana da kungiyar kasashen gabashin Afirka

Abdoulaye Mamane Amadou
January 20, 2024

Gwamnatin mulkin sojan Sudan ta sanar da janyewa kwata-kwata daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yankin gabashin Afirka.

https://p.dw.com/p/4bV1F
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Sudan Janar Abdel Fattah Al-Burhan
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Sudan Janar Abdel Fattah Al-BurhanHoto: Sudanese Army/AFP

Matakin Sudan baya rasa nasa da ganawar da shugabannin kungiyar suka yi da janar Mohammed Hamdane Daglo, babban abokin hamayyar shugaba Abdel Fattah al-Burhan, a kokarin da suke na sulhunta rikicin bangarorin biyu.

Sojojin da ke biyayya ga Janar Daglo na fafata yaki da dakarun sojan Sudan a kokarinsu na karbe iko daga gwamnatin al-Burhan.

A yayin taro da kungiyar ta gudanar karo na 42 a wannan Alhamis, kungiyar Igad ta kasahen yankin Gabashin Afirka ta gana da tsohon firaministan gwamnatin farar hulla Abdallah Hamdok, a kokarinsu na samun mafita kan yakin basasa a Sudan, lamarin da ya fusata gwamnatin Janar al-Burhane.