1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Sudan a gaban kuliya

Zulaiha Abubakar
July 21, 2020

Gwamnatin Sudan ta kebe Talatar wannan makon, a matsayin ranar da za a fara shari'ar hambararren shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir wanda ya jagoranci juyin mulkin da ya kai shi ga shugabancin kasar na shekaru 31.

https://p.dw.com/p/3fdkb
Gipfeltreffen der Arabischen Liga in Doha Omar Hassan Al Bashir
Hoto: picture-alliance/abaca/A. A. Rabbo

Daga laifuffukan da ake tuhumarsa akwai yiwa dokokin tsarin mulkin kasar karan tsaye kamar yadda guda daga cikin lauyoyin da suka shigar da karar ya shaidawa manema labarai a wannan Talatar. Tsohon shugaba al-Bashir mai shekaru 76 zai gurfana gaban shari'ar ne tare da wasu mutane 60 da suka hada wasu wadanada suka rike mukaman mataimakan shugaban kasar da tsoffin ministoci da kuma tsoffin gwamnoni a lokacin gwamnatinsa.