1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki ya tilasta mutane sun fice daga Sudan

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 20, 2023

Shugaban Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majamisar Dinkin Duniya Filippo Grandi ya bayyana cewa, fiye da mutane dubu 500 ne suka tsere daga kasar Sudan sakamakon yakin da ke faruwa.

https://p.dw.com/p/4SpsX
Sudan | Filippo Grandi | Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Salvatore Di Nolfi/KEYSTONE/picture alliance

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majamisar Dinkin Duniya ta kara da cewa wasu mutanen kimanin miliyan biyu sun zama 'yan gudun hijira na cikin gida. Filippo Grandi ya fadi haka ne, yayin taron manema labarai a birnin Nairobi na kasra Kenya. Hukumar ta ce ana bukatar makudan kudi domin taimakon mutanen da suka tagayyara sakamakon yakin. Yaki ya barke a Sudan tun ranar 15 ga watan Afrilu, tsakanin bangaren Janar Abdel Fattah al-Burhan shugaban gwamnatin wucin gadin kasar da kuma mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo shugaban rundunar mayar da martani ta RSF.