1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Mayakan RSF sun shiga Wad Madani

Abdullahi Tanko Bala
December 19, 2023

Akalla mutane 300,000 aka yi kiyasin sun tsere daga jihar El Gezira ta Sudan sakamakon dauki ba dadi tsakanin sojojin sa kai na RSF da rundunar sojin gwamnatin Sudan a cewar kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM

https://p.dw.com/p/4aKLB
Sudan | Sojoji a birnin Gedaref a gabashin Sudan
Hoto: AFP/Getty Images

Tun watanni takwas da suka gabta dakarun sa kai na RSF suke dannawa Wad Madani babban birnin jihar El Gezira kuma a ranar litinin mayakan suka shiga birnin a cewar rahotanni.

Yaki tsakanin sojoji da RSF ya tilasta wa mutane fiye da miliyan bakwai barin gidajensu yayin da a waje guda halin tagaiyarar da jama'a suka shiga ya haifar da kashe kashen kabilanci a Darfur.