1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar Sudan ta dauki sabon salo

Ramatu Garba Baba
April 6, 2019

'Yan sanda sun yi anfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi yunkurin shiga hedkwatar sojoji da fadar gwamnati don ganin sun tilasta wa Shugaba Omar al-Bashir yin murabus daga mukaminsa.

https://p.dw.com/p/3GPSR
Sudan Weiterhin Proteste |
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Tun da safiyar wannan Asabar, dubban masu zanga-zanga suka soma yin maci a babban birnin kasar Kahrtoum, inda da yawa daga cikinsu suka kai hedlkwatar rundunar sojan kasar, wanda shi ne tattaki irinsa na farko tun bayan fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaban al-Bashir a shekar bara.

Masu zanga-zangar da suka yi dafifi a sansanin sojin kasar da ke birnin Khartoum da fadar shugaban kasar sun mayar da martani da jifan 'yan sandan da suka nemi hana su shiga. An dai zabi wannan rana ta yau wato 6 ga watan Afrilu ta zama ranar maci na kasa baki daya don a ranar ce a shekarar 1985 wani juyin mulki ya kifar da gwamnatin Shugaba Jaafar Nimeiri.