1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nemat ta zama babbar alkalin Sudan

Abdul-raheem Hassan
October 11, 2019

Majalisar mulkin kasar Sudan ta nada mace a karon farko a mastayin babbar alkalin kasar bayan matsin lamba 'yan fafutuka na ganin an kori ma'aikatan gwamanatin Omar al-Bashir.

https://p.dw.com/p/3R6j8
BG Frauen im Sudan
Hoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

Nemat Abdullah Khair shararriyar lauya ce da ta shafe kusan shekaru 40 tana aikin alkalanci a Sudan, kuma ta kasance mace ta farko da ta fara rike mukamin babban alkali a kasar.

Kakakin gwamnatin hadakar soji da ta farar hula a Sudan Mohammed al-Fakki Solimon ya ce an tabbatar da Taj al-Ser Ali al-Hebr a matsayin babban mai shigar da kara. A watan Afirilun shekarar 2019 ne aka kawo karshen gwamnatin Omar al-Bashi na tsawon shekaru sama da 30, bayan jerin zanga-zangar neman sauyin gwamnati.