1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki na ci gaba da daidaita Sudan

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 8, 2023

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Sudan ta bayyana cewa kimanin mutane 22 ne suka halaka yayin da wasu da dama suka jikkata, sakamakon harin jiragen yaki da sojojin kasar suka kai a yammacin birnin Omdurman.

https://p.dw.com/p/4Tcnx
Sudan | Yaki | Sojoji | 'Yan Tawaye | RSF | Omdurman
Har yanzu ana ci gaba da gwabza fada a SudanHoto: Mostafa Saied/REUTERS

Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da yakin da ake gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawayen RSF ke shiga mako na 12. Sojojin na RSF dai sun mamaye Khartoum babban birnin kasar da biranen Omdurman da Bahri, bayan da fada ya barke tsakaninsu da dakarun gwamnatin mulkin sojan kasar a ranar 15 ga watan Afirilun wannan shekara da muke ciki. An dai yi ta kokarin sasanta bangarorin biyu ba tare da cimma nasara ba, abin da ke janyo fargabar fadawar kasar cikin gagarumin yakin basasa. Tuni dai an fara samun wadanda ke shiga cikin yakin a ciki da wajen kasar da ke yankin gabashin Afirka, wadda kuma ke tsakanin yankin Kahon Afirka da yankin Sahel da kuma Tekun Maliya.