1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Hankula sun kwanta a Darfur

January 19, 2021

Dakarun gwamnati a Sudan sun dawo da kwanciyar hankali a yankin Darfur na kasar, bayan kwashe kwanaki uku ana rikici tsakanin kabilu da ya yi sanadin rayukan kimanin mutum 155.

https://p.dw.com/p/3o8A7
Sudan | Protest | Militär in Khartoum
Hoto: Reuters/U. Bektas

Gwamnatin rikon kwarya a babban birnin kasar Khartoum ce ta tura da rukunin sojoji zuwa yankin, inda hukumomi suka nuna fargabar karin zubar da jini.

Tun dai a ranar Asabar din da ta gabata ce dai rikici ya barke a tsakanin makiyaya labarawa da kuma mambobin wata kungiyar kabilar a El Geneina da ke yammacin Darfur, wanda ya yi sanadin rayukan kimanin mutane 155, yayin da wasu 130 suka jikkata. Haka kuma mutane kimanin dubu hamsin suka rasa matsugunansu sanadiyar rikicin. Rikicin dai ya zo a dai-dai lokacin da dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke shirin janyewa daga yankin baki daya.

Tuni dai mahukunta yammacin Darfur, suka sanya dokar hana zirga-zirga yayin da jami'an soji suka isa yankin da ma wasu jihohin don dawo da kwanciyar hankali.