1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Amirka za ta bude ofishin jakadanci

Mahmud Yaya Azare AAI
December 5, 2019

A karon farko bayan shekaru 23 Amirka da Sudan za su dawo da huldar jakadanci, da ta kai ga batun bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu, lamarin da ya jawo fashin bakin masana da mayar da martanin 'yan kasar ta Sudan.

https://p.dw.com/p/3UHLy
Mike Pompeo a ofishin jakadancin Amirka
Mike Pompeo a ofishin jakadancin AmirkaHoto: picture-alliance/dpa/AP/M. Altaffer

Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ambaci jerin dalilai shida, da ta dogara da su wajen dawo da cikakkiyar huldar jakadanci da kasar Sudan, kamar yadda sakataren Amirka Pompeo ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Khaled Khairy, jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Sudan, na daya daga cikin wadanda suka kawo wadan nan dalilai:
"Sun yaba da kamun ludayin firam minister Abdalla Hamdok, wanda ya yi nasara zuwa yanzu, kan yadda yake tafiyar da kasar. Dage takunkumi ga 'yan jaridu da kungiyoyi masu zaman kansu, da shiga tattaunawa ba tare da gindaya sharudda ba ga kungiyoyin 'yan tawaye mabanbanta da ke dauke da makamai, da kuma gudanar da tsarin mulkinsa, ba tare da kumbiya-kumbiya ba, gami da sakar wa gidan shari'a mara, ya yi aikinsa kan doka, ba tare da samun katsalandan daga sama ba, da kuma uwa uba yadda yake bin taswirar kan hanyar mika mulki ga farar hula sau da kafa, wanda zai kare cikin tsukun watanni 36."
Wannan matakin dai na zuwa ne, a daidai lokacin da firam ministan na Sudan Abdallah Hamdok, ke ziyarar aiki a birnin Washinton na Amirkan, wanda ya fada wa 'yan jarida cewa, bai dace ba a ci gaba da dora wa al'ummar Sudan laifukan da ba su san hawa ko sauka kansu ba:

Sabon firam ministan Sudan Abdalla Hamdok
Sabon Firam ministan Sudan Abdalla Hamdok Hoto: picture-alliance/AP Photo

"Mu a gwamnatin rikon kwarya ta Sudan, muna kira da babbar murya ga Amirka da ta cire Sudan daga jerin kasashe masu goyan bayan ta'adanci a duniya. Rashin adalci ne aci gaba da gallaza wa al'ummar Sudan kan laifukan da shuwagabanninsu da sukai ta gasa musu aya a hannu suka tafka ba.''
Tun a shekarar 1994 ne dai Amirka ta sassauta wa Sudan a takunkumin tattalin arzikin da ta kakaba mata, sakamakon fara tattaunawar da ta shiga yi, da 'yan tawaye masu dauke da makamai, amma ba ta cire sunanta daga cikin jerin kasashen da ke tallafa wa 'yan ta'adda a duniya ba, wanda Amirka ta sanya Sudan tun a lokacin da ta ke baiwa Bin Laden mafaka.
A yayin da 'yan kasar ta Sudan ke lale marhabin da wannnan matakin da suke ganin zai rage radadin matsanancin karayar tattalin arzikin da suke fama dashi, wasu masu fashin baki a kasar irin su, Muhyeedden Tareeq, na kira da a rage zumudi, kafin aga fada da cikawa na Amirkan:
''Soke sunan Sudan daga jerin kasashen da ke goyon bayan ta'addanci a duniya, na bukatar amincewar 'yan majalisar Amirka, wadanda a yanzu suka shagaltu da harkokin zabe. Don haka a gaskiya dole mu yi taka tsantsan, har sai munga yadda lamura suka kaya a Washinton.

Shugaban Amirka Donald Trump da sakataren wajen Amirka Mike Pompeo
Shugaban Amirka Donald Trump da sakataren wajen Amirka Mike PompeoHoto: AFP/B. Smialowski