1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka tsakanin masu borai da sojoji a Sudan

Abdourahamane Hassane
June 9, 2019

Shugabannin da ke jan ragamar borai a Sudan sun yi kira ga jama'a da kada su martaba dokokin kasar har sai abin da hali ya yi.

https://p.dw.com/p/3K5lK
Sudan | Streik
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Likitoci na kusa da masu yi boran sun ce sama da mutane 100 suka rasa rayukansu wasu 500 suka jikata, galibi a lokacin da jami'an tsaro suke tarwatsa masu gangamin. Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da firaminista Habasha  Abiy ahmed ya kammala ziyarar da ya kai a Sudan din  domin shiga tsakani a rikicin tsakanin sojojin da masu yin zanga-zanga.