1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin sabuwar zanga-zanga a Sudan

Mahamud Yaya Azare LMJ
June 10, 2021

Kwana guda bayan da mahukuntan Sudan suka janye tallafin man fetur, kungiyar kwadagon kasar ta yi kira da a fara zanga-zanga domin tilasta wa mahukunta janye matakin.

https://p.dw.com/p/3ujGy
Sudan Premierminister Abdalla Hamdok
Firaministan Sudan Abdalla HamdokHoto: Hannibal Hanschke/Reuters

Gwamnatin ta Sudan dai ta kammala janye ilahirin tallafin man fetur da dangogin nasa wanda ta ke shigarwa daga ketare, matakin da ya janyo ninkuwar farashinsu da ma karancinsu a kasar. Tashar talabijin ta Algad, ta nuna yadda aka samu dogayan layuka a gidajen man fetur din birnin Khartum, inda  farashin man fetur din ya tashi daga fam 150 zuwa 290, shi kuma dizel ya koma fam 285 daga 125 da ake sayarwa a baya.

Karin Bayani: Sojojin Sudan sun yi harbi a asibiti

Manistan  kudin kasar Jibril Ibrahim da ke sanar da matakin ya ce Sudan na kashe biliyoyin daloli wajen biyan tallafin kowacce shekara, a yayin da galibin 'yan kasar ba sa cin moriyar wannan tallafin. A cewarsa a kan wannan dalilin, yanzu za a karkata akalar tallafin zuwa ga noma da samar da lantarki da gina hanyoyi a kasar. Wannan matakin dai na zuwa ne makwanni kalilan bayan da kasar ta Sudan ta cimma yarjejeniya da Asusun ba  da Lamuni na Duniya IMF, na karbar bashi a kokarin da suke na tayar da komadar tattalin arzikin kasar.

Sudan I Geldscheine I Markt von Khartoum
Farashin man fetur ya tashi, bayan janye tallafin man fetur din a SudanHoto: Hussein Malla/AP/picture alliance

Tuni dai Kungiyar kwadago ta Sudan ta yi kira ga 'yan kasar da su fito su yi zanga-zanga domin nuna adawa da janye tallafin. Mahjub Dasuki shi ne kakakin 'yan kwadagon: "Ba mu kama hanyar gyara ba, mun kama hanyar kara lalata lamura ne. Kamar yadda karya darajar kudiunmu da asusun ya sanya muka yi bai tsinana mana komai ba in ban da karawa talakawa wahala, shi ma wannan janye tallafin babu abin da zai yi sai halaka kasa da talakawanta."

Karin Bayani: Gangamin neman demokradiyya a Sudan

Wasu da ba sa adawa da janye tallafin dai sunce da kamata ya yi ai taka tsan-tsan wajen janye shin. Da ma dai a farkon makon nan ne aka jiyo mataimakin shugaban kasar ta Sudan Mohamed Hamdan Dagalo wanda ke da burin cire kaki ya shiga siyasa domin ya tsaya takara a zaben da ke tafe, yana suka ga yadda ya ce gwamnatin rikon kwaryar kasar ke tafiyar da lamuranta: "Yanzu akasar nan muna cikin wani mummunan yanayi.Talaka kai hatta masu kudin sai sake shan wahala suke yi. Babu wani chanjin da aka samu in banda kifar da gwamnatin Omar al-Bashir. Domin duk wadanda ke rike da madafun iko, babu wanda ke son ayi sauyi na hakika.."