1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain jam'iyyar masu kyamar baki na iya taka rawar gani

Abdourahamane Hassane
April 26, 2019

Shugaban gwamnati na jam'iyyar masu ra'ayin gurguzu a Spain Pedro Sanchez ya yi gargadin cewar akwai barazanar cewar jam'iyyar masu kyamar baki za ta samu babban kaso a zaben da za a yi na ranar Lahadi(28-04-19).

https://p.dw.com/p/3HVj8
Spanien Sevilla Wahlkampfauftritt von Santiago Abascal
Hoto: Getty Images/AFP/C. Quicler

Pedro Sanchez ya ce a hasashen da aka yi da farko na nuna cewar jam'iyyar VOX za ta samu kishi goma cikin dari na kuri'un da za a kada. Sai dai ya ce akwai bazata sakamakon yada a kwana baya a Finland ba zato ba tsammani jam'iyyar masu kyamar baki ta zo ta biyu a zabukan kasar.