1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSpaniya

An yi wa sarkin Spain da firaminista kuwa a Paiporta

Abdourahamane Hassane
November 3, 2024

Al'umma ta jefa wa Sarki Felipe VI da Sarauniya Letizia da kuma firaminista Sánchez laka a fuskokins a Paiporta, a lokacin ziyara da suka kai ta gani da ido a yankin da ambaliya ta shafa.

https://p.dw.com/p/4mXt4
Hoto: Manaure Quintero/AFP/Getty Images

 Sarki Felipena shidda na Spain da sauraniya Letiza da firaminista Pedro Sánchez za su kai ziyara a kudu maso gabashin Spain inda ake sa ran za a sake samun ruwan sama kamar da bakin kwarya bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta yi sanadin mutuwar mutane akalla   217.Kwanaki biyar bayan wannan mummunan yanayi da ya haifar da iftala'i mafi muni a tarihin kasar a cewar gwamnati, Ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka bace, tare da share hanyoyin da kuma dawo da ababen more rayuwa da kogin laka ya lalata. Wannan ziyarar tasu ta zo ne a daidai lokacin da hukumar kula da yanayi ta kasar Spain  ta fitar da wani sabon hasashe na  ruwan sama mai karfi a yankin  Valencia.