Sosomin lafawar kura a Siriya
January 2, 2012Kungiyar kasashen Larabawa ta ba da sanarwar janye dakarun gwamnati daga unguwanin da ake gudanar da zanga-zanga a cikinsu a kasar Siriya inda hakan ke ma'anar sosomin tafarkin samar da zaman lafiya. A cikin jawabin da ya yi a birnin Alkahira na kasar Masar, babban sakataren kungiyar Nabil al Arabi ya ce yanzu sojoji sun janye zuwa wajen birane. To sai dai har yanzu akwai 'yan bindiga da ke ci gaba da yin barazana.
Da farko dai an soki tawagar 'yan sa ido ta kungiyar kasashen Larabawa a dangane da tashin hankalin da aka ci gaba da fuskanta a daiden lokacin da take ziyara a kasar -dalilin da sa ya wani komiti na masu fada a ji a kungiyar ya bukaci dakatar da aikin tawagar ba da bata wani lokaci ba. Komitin mashawartan kungiyar mai mambobi 88 ya ce ci gaba da fuskantar tashin hankali a ma lokacin da tawagar ke ziyara a Siriya na maanar ba da goyon baya ga shugaba Bashar Al Assad.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal