1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a gudanar da zaben kasar Somaliya

Binta Aliyu Zurmi
May 5, 2022

A ranar 15 ga wannan wata na Mayu da muke ciki ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Somaliya, a cewar sanarwar da kwamitin gudanar da zaben kasar ya fidda a yau.

https://p.dw.com/p/4AtDL
Somalia Präsident Farmajo Premierminister Roble
Hoto: Abdirahman Yusuf/AFP/Getty Images

Zaben da ke tafe bayan jinkiri na kusan shekara guda da aka samu, za a fafata ne a tsakanin shugaba mai barin gado Mohammad Abdullahi Mohamed Farmanjo da kuma firaminista Mohamed Hussein Roble.

Kasashen duniya gami da kungiyoyi sun taimaka wajen ganin an gudanar da zabe a kasar ta Somaliya da ke fama da matsaloli ko baya ga na siyasa da ma na ayyukan kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai.

Ana fatan wannan zabe da ke tafe ya kawo karshen rigingimu da kasar ke fama da shi musamman na baya-bayan nan hare-haren mayakan Al-shabab da suka kai ga rasa wasu 'yan siyasa biyu.