1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar siyasa a Somaliya a gabanin babban zabe

Abdul-raheem Hassan AMA
December 30, 2020

'Yan adawa a Somaliya sun yi barazanar kauracewa zaben shugaban kasa da hukumar zabe ta shirya a watan Fabrairun 2021, bayan dage ranar zaben ta ainihi na watan Satumba.

https://p.dw.com/p/3nNWV
Russland Sochi | Präsident Somalia | Mohamed Abdullahi Mohamed
Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed Hoto: Vladimir Smirnov/Imago Images

Fargabar sabon rikicin siyasa ya sake ta'azzara a Somaliya bayan da 'yan takarar shugaban kasa suka yi hadaka ciki har da tsoffin s hugabannin kasar biyu, inda suka yi baraznar kauracewa shiga zaben da hukumar shirya zaben kasar ta sa a watan Fabrairun 2021.
'Yan adawar na zargin shugaban kasa a Somaliya Mohamed Farmajo da yunkurin tsawaita wa'adin mulki na wasu shekaru hudu.

Sun kuma yi zargin cewa wadanda za su shirya zaben duk mabiya gwamnatin kasar ne. Ridwan Hersi, kakain gamayyar jam'iyyun adawa "ya ce gwamnatin ta yi watsi da kiraye-kirayen garanbawul a kwamitin shirya zaben, don haka, mun yanke hukuncin hada babban kwamitin shirya zabe na kasa wanda zai yi aiki da mu bisa gaskiya da adalci a kasar nan. Muna kira ga gwamnati da ta guji kirkiro yanayin da za a gudanar da zabe mara gaskiya."

Karin Bayani:An kai harin kunar bakin wake a Mogadishu

Somalia Ministerpräsident Mohamed Hussein Roble
Mohamed Hussein Roble minista a SomaliyaHoto: Sadak Mohamed/AA/picture alliance

Ministan shari'ar Somaliya Salah Jama ya ce gwamnati ta shirya gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana ta yadda kowane zai amince da tsarin yadda zaben zai gudana. Manzo na musamman da Amirka ta tura a Somaliya Donald Yammato, ya taka rawa sosai a yankin kahon Afirka ya bayyana cewa "Kasashen waje ba su taba yarda da wani tsarin zabe na daban da 'yan adwar ke shirin gudanar ba, Amirka da sauran hukumomi da kungiyoyi sun damu da tsarin zaben, muna kira ga gwamnatin da ta warware matsalar banbance-banbancen da ake fuskanta."

A Somaliya, wakilai ke zaban 'yan majalisa, sannan 'yan majalisa su zabi shugaban kasa, tsarin da ke shan suka da zargin cin ahnci da sayan kuri'un mata da matasa.