1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soke shari'a a Libiya

December 26, 2005

Kotun Koli ta Libiya ta soke hukuncin kisan da aka yanke wa wasu fursinoni su shida

https://p.dw.com/p/Bu33
Libiya
LibiyaHoto: dpa

Tun da farko dai sai da aka cimma daidaituwa tsakanin fadar mulki ta Tripoli a bangare guda da kasashen Amurka da Bulgariya da KTT a daya bangaren akan kirkiro wani asusun taimako na kasa da kasa domin amfanin yaran da suka kamu da cutar ta Aids. To sai dai kuma soke hukunci da kuma mayar da shari’ar hannun wata ‚yar karamar kotu baya nufin cewar za a kakkabe su ne kwata-kwata daga laifin da ake zarginsu da shi. Tun a cikin watan janairun shekara ta 1999 ne aka tsare fursinonin su shida a gidan kutkuku, bisa zarginsu da yada kwayoyin cutar Aids a tsakanin yara 425 a wani karamin asibiti a Libiya. Tuni wasu sama da 50 daga cikin yaran suka yi asarar rayukansu. Sai dai fursinonin su sha musunta wannan zargi da ake musu. Wasu kwararru na kasa da kasa abin da ya hada har da Luc Montagnier, daya daga cikin gaggan masanan da suka gano kwayar cutar ta Aids sun ba da shaidar cewa, wadannan yara a asibitin yara na Fatah dake Bengasi, sun kamu da kwayoyin cutar ne sakamakon rashin tsafta. Wasu daga cikin yaran sun kamu da cutar ne tun kafin nes-nes din daga Bulgariya su kama aikinsu a asibiti, wasu daga cikinsu kuma sai bayan da su kansu nes-nes din suka kamu da kwayar cutar. Bugu da kari kuma fursinonin sun bayyanar a fili cewar sun amince da laifin da ake zarginsu da shi ne sakamakaon azabtar da su da aka yi. Amma duk da haka an yanke musu hukuncin kisa a cikin watan mayun shekara ta 2004, su kuma wadanda ake zarginsu da laifin azabtar da fursinonin an sakesu a shari’ar da aka yi musu a cikin watan yunin da ya wuce.

A yanzun kuma ba zato ba tsammani kotun koli ta kasar Libiya ta soke hukuncun kisan sakamakon wasu kura-kurai da ta ce an caba a zaman shari’ar sannan ta danka alhakin sake kama shari’ar a hannun wata kotun miyagun laufika dake Bengazi. Amma ga alamu dalilin tsayar da wannan shawarar shi ne daidaituwar da aka cimma tsakanin Libiya da Bulgariya a ‚yan kwanakin baya-bayan nan a game da kafa wani asusun taimako ga yaran masu kwayoyin HIV. Kazalika kasashen Turai da Amurka sun sake yin wa gwamnatin shugaba Gaddafi matsin lamba.