1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Neman sasanta rikicin Sudan

Suleiman Babayo USU
October 25, 2023

Sojojin Sudan sun tabbatar da cewa sun amince amsa goron gayyata domin komawa kan teburin sulhu na neman shawo kan yakin da ya barke a kasar.

https://p.dw.com/p/4Y1Do
Sudan | Janar Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan da Mohamed Hamdan Dagalo
Janar Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan da Mohamed Hamdan DagaloHoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

A wannan Laraba rundunar sojan Sudan ta bayyana amincewa da karbar goron gayyata zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya domin kammala tattaunawa batun zaman rundunar mayar da martani inda bangarorin suka kwashe watanni suna kai ruwa rana. Yakin ya barke sakamakon sabani tsakani Janar Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhanshugaban gwamnatin sojan da mataikinsa Mohamed Hamdan Dagalo na rundunar mayar da martani.

A cikin wata sanarwa rundunar sojan Sudan ta tabbatar da batun komawa kan teburin tattaunawar. Kasashen Amirka da Saudiyya suke daukan nauyin wannan tattaunawar domin shawo kan yakin da ya barke a kasar ta Sudan tun tsakiyar watan Afrilu.