An saki masu adawa da mulkin soji a Sudan
November 23, 2021Matakin sako gwamman yan adawar dai wani bangarene na yarjejeniyar da aka cimma tsakanin jagoran juyin mulkin sojin kasar,Janar Abdel Fattah Burhan, da Hambararen firaim ministan kasar da aka sake mayar dashi kan makaminsa, Abdallah Hamdok.
Jagoran jam'iyyar Sudan Congress Party Omar al-Degeir, na daya daga cikin mutanen da aka sallama bayan kama shi a ranar 25 ga watan Okotban da ya gabata lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin firaminista Hamdok. ya kuma sanarwa 'yan jarida cewa, ya yi ammanar cewa, matsin lambar masu zanga-zanga ce takai ga sako shi ba wai yarjejeniyar da Hamdok ya cimma da Burhan ba.
To sai dai kamar yadda Adam Isa na kungiyar Justice and Equality Front ke cewa, har abada, babu ta yadda za a samu mafita a rikicin siyasar kasar, muddun za a ci gaba da dora wa juna laifin kiki-kakar siyasar da ta barke a kasar.
A daura da haka, kungiyoyin juyin-juya halin da aka yi wanda ya kai ga kifar da gwamnatin Shugaba Umar al-Bashir, sun kafa wata gamayyar matsin lamba mai suna Change and Freedon Force, don sa ido ga sabuwar gamin gambizar da Hamdok zai sake kafawa, da zimmar tabbatar da cewa, ba a bai wa manufofin juyin-juya hali a kasar dan waken zagaye ba.