1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Siriya sun killace garin Jisr a-Shugur

June 13, 2011

Gidan telebijin na ƙasar Siriya ya bayyana cewar garin Jis al-Shughur ya koma ƙarƙashin kulawar gwamnati bayan da sojoji suka yi amfani da ƙarfi domin murƙushe boren neman sauyi.

https://p.dw.com/p/11ZH7
Lokacin da Sojojin Syriya suka isa garin Jisr al-ShughourHoto: dapd

Sojojin ƙasar Siriya na ci gaba da amfani da tankokin yaƙi da jiragen masu saukar ungulu da kuma bindigogin iggwa a Jisr al-Shughur, domin murƙushe boren neman sauyi da garin yayi ƙaurin suna akai a idanun gwamnati. Gidan  talabijin ɗin ƙasar ya ce dakarun gwamanti sun yi nasarar mayar da garin ƙarƙashin kulawarsu bayan da suka shafe sa'o'i suna fafatawa da 'yan bindiga da suka ja daga. Kanfanin dillacin labaran Anatolie ya ruwaito cewar kimanin 'yan Syriya dubu biyar ne suka tsere daga ƙasar zuwa Turkiya domin tsira da rayukansu.

Masu rajin kawo sauyi sun bayyana cewar mutane aƙalla 1.300 ne suka rasa rayukansu tun bayan ƙaddamar da zanga-zangar ƙin jinin gwamanti watannin uku ke nan da suka gabata. Sai dai ƙungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ƙiyasta cewar mutane 1.100 ne suka rigamu gidan gaskiya. Ya zuwa yanzu dai babu wata kafa da ta tabbatar da waɗannan alƙaluma sakamakon haramta wa manaima labaru shaidar da yadda guguwar neman sauyin ke kaɗawa a Siriya da kukumomi ke yi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi