1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Siriya sun kashe masu zanga zanga

May 20, 2011

Mutane guda biyar suka mutu sakamakon buɗe wuta da bindigogi da jami'an ƙwantar da tarzoma suka yi akan jama'a a garin Homs

https://p.dw.com/p/11KS3
Ana ci-gaba da gudanar da zanga-zanga ƙin jinin gwamnati a garin HomsHoto: picture alliance/dpa

jami'an tsaro a ƙasar Siriya sun buɗe wuta da harsashai na gaske ga masu yi borai wanda suka gudanar da gangami bayan sallah juma'a a garin Homs da ke a yanki arewa maso gabaci, wanda kuma shi ne birnin na ukku ma fi girma na ƙasar. Mutane biyar suka rasa rayukan su ɗaya daga cikinsu yaro ,yayin da ɗaya ya mutu a yankin kudanci a garin Sanamein.

Rahotanni na cewar an gudanar da zanga zanga a garuruwa da dama na ƙasar akan kiran da yan adawar suka yi.A garin Banias jama'ar sun gudanar da marchi kusan babu riguna a jiginsu domin nuna cewar basu ɗauke da makamai kamar yadda gwamnatin ke zargin su .

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman