1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi sojin Najeriya da zubar wa mata 10,000 ciki

December 8, 2022

Kamfanin Reuters ya ce ya bankado yadda sojojin suka zubar wa da akalla mata 10,000 juna biyun da suka samu a sakamakon fyade ko auren dolen da 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi suka yi musu.

https://p.dw.com/p/4KdiY
Hoto: DW/F. Muvunyi

Wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gudanar ya bankado yadda rundunar sojin Najeriya ke aiwatar da wani shiri na musamman na zubar wa da mata ciki tun daga shekara ta 2013.

Reuters ya ce ya samu gamsassun bayanai daga wasu 'yan matan da aka zubar wa da cikin da malaman asibitin da suka yi aikin da sauran masu masaniyar wannan shiri, da hujjoji suka nuna an gudanar da shi a asirce.

Sai dai kuma rundunar sojin ta Najeriya ta mayar da martani da kakkausan lafazi ga wannan rahoto da aka fitar a ranar Laraba, tana mai cewa babu wani abu da ke cikin zargin na Reuters in ba cin fuska ga 'yan Najeriya ba.

Sojojin da suka fito karara suka nuna rashin wanzuwar wannan lamari, sun ce jami'ansu sun yi wayewar da ba za su amince a zubar da ciki a kowane bangare na Najeriya ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.