1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dakarun wanzar zaman lafiya sun mutu a Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
June 4, 2022

A Mali wasu sojin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya biyu sun gamu da ajalinsu sakamakon taka nakiya da motar ta yi a yankin Douentza na tsakiyar kasar.

https://p.dw.com/p/4CHTi
Mali | MINUSMA | Friedenstruppen | UNPOL
Hoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/IMAGO

Da yake ganawa da manema labaru kakakin rundunar sojan MINUSMA Olivier Salgado, ya ce hatsarin da faru a yankin Douentza da ke tsakiyar Mali da ya hallaka 'yan kasar Masar biyu, tare da raunata wasu dakarun rundunar biyu, kana harin na zuwa ne bayan da wani sojin rundunar dan kasar Jodan daya yace ga garinku sakamakon wani farmakin roka da 'yan ta'addata suka kai wa ayarin sojan MINUSMA a yankin Kidal da ke arewacin Mali.

Ko baya ga sojin na Majalisar Dinkin Duniya wasu fararen hula shida sun gamu da ajalinsu sakamakon taka nakiya a yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga cin kasuwa a wani gari mai suna Waya.

Wannan ne karo na shida da 'yan bindiga ke kai hare-hare kan dakarun rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya daga ranar 22 ga watan jiya zuwa wannan wata.

Tuni ma shugaban rundunar El-Ghassim Wane da ma babban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya duk sun yi Allah wadarai da harin, suna masu cewa hakan ka iya dagula yunkurin da rundunar ke yi na ganin an samu zaman lafiya.