1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Masar ba za su far wa masu bore ba

Umar Saleh SalehJanuary 31, 2011

Rundunar sojojin Masar ta ce ba za ta yi amfani da tsinin bindiga ko kuma ƙarfin tuwo ba wajen tarwatsa mutane miliyon ɗaya da za su gudanar da zanga-zanga a ranar talata a birnin Alƙahira

https://p.dw.com/p/1085e
Jan dagan masu zanga-zanga a MasarHoto: picture-alliance/dpa

Masu zanga-zangar neman hamɓarar da jagorancin shugaba Hosni Mubarak na ƙasar Masar sun yi ƙira a gudanar da gagarumin gangami a wannan talata domin hamɓarar da Hosni Mubarak daga mulki. Wannan yunƙurin ya zo ne a dai dai lokacin da suke ci gaba da gudanar da jerin gwanon su na mako guda kenan a jere.

Shagunan sayar da kayayyaki da dama ne suka kasance a rufe, a yayin da kamfanonin ƙetare kuma suka ci gaba da dakatar da ayyukan su sakamakon rikicin siyasar da ke faruwa a ƙasar. Sai dai sojojin ƙasar suka ce ba za su yi amfani da ƙarfi ba wajen tarwatsa masu zanga-zanga a gobe.

'Yan yawon buɗe ido da dama ne kuma suka rungumin jakunkunan su tare da nufar babban filin saukar jiragen saman birnin al-Qahira - a ƙoƙarin su na ficewa daga ƙasar. A halin da ake ciki kuma tashar telebijin na Aljazeera ta sanar da cewar hukumomin ƙasar ta Masar sun saki ma'aitanta guda shidan da suka tsare bisa zargin nuna son kai wajen bayar da rahotanni game da zanga zangar, inda kuma al'ummar ƙasar ke shirin gudanar da jerin gwanonn da zasi sami halartar miliyan 'yan ƙasar a wannan Talatar.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Halimatu Abbas