1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Mali sun kashe wani jigo a kungiyar IS

April 30, 2024

Rundunar sojin Mali ta yi ikirarin kashe wani babban jigo na kungiyar masu da'awar jihadi ta IS wanda tun da jimawa Amurka ta sanya tukwici a kansa.

https://p.dw.com/p/4fKwi
Mali | G5 Sahel Militärallianz
Hoto: Hans Lucas/IMAGO

Gidan talabijin mallakar gwamnatin Mali ya ruwaito cewa an halaka kasurgumin dan ta'addar mai suna Abou Houzeifa a yayin wasu samame da sojojin kasar suka kai a ranar Lahadin da ta gabata a yankin Meneka da ke Arewa maso gabashin kasar.

Karin bayani: 'Yan ta'adda sun kai hare-hare a wasu sansanonin sojan Mali

Shi dai Abou Houzeifa da ake kira Hugo ya kasance daga cikin wadanda suka tafka cin zarafin fararen hula a kasashen yankin Sahel, sannan kuma yana da hannu a harin kwantan baunar da ya yi ajalin sojojin Amurka hudu da na Nijar biyar a Tongo Tongo a shekarar 2017, har ma Washington ta saka tukwicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya yi nasarar kamo mata shi.

Karin bayani: Rundunar tsaron hadin gwiwa a kasashen AES

Wata majiyar tsaro a Mali ta ce sojojin kasar sun samu tallafin abokan huldarsu na Rasha wajen gano mabuyar Abou Houzeifa da mayakansa da ke kai hare-hare da babura kafin daga bisani su fatattake su.