1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Mali sun ce sun gano kabari na bai daya a Kidal

Mouhamadou Awal Balarabe
November 19, 2023

A cikin wata sanarwar da ta fitar a Bamako, rundunar sojin Mali ta ce kabarin na nuna irin ta’asar da wadanda ta danganta da marasa imani suka aikata, amma ba tare da bayar da karin bayani ba.

https://p.dw.com/p/4Z96p
Sojojin Mali sun juma da fara sintiri a arewacin kasar sakamakon matsalar tsaro
Sojojin Mali sun juma da fara sintiri a arewacin kasar sakamakon matsalar tsaroHoto: Getty Images/AFP/M. Cattani

Rundunar sojin Mali ta ce ta gano wani kabari na bai daya a Kidal da ke yankin Arewa maso gabashin kasar, mako guda bayan kwato garin daga hannun Abzinawa 'yan tawaye. A cikin wata sanarwar da ta fitar a Bamako, rundunar ta ce kabarin na nuna irin ta'asar da wadanda ta danganta da marasa imani suka aikata, amma ba tare da bayar da karin bayani ba.Karin bayani: 

Dakarun Mali sun kwace Kidal

Hukumomin na Mali sun bayyana cewar suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda ke hannu a kashe-kashen domin hukunta su. Tun a  ranar 14 ga watan Nuwamba ne, Mali ta yi nasarar mayar da Kidal karkashin ikonta shekaru tara bayan da ta kasance tungar 'yan awaren Abzinawa wadanda suke bijerwa wa hukumomin Bamako.