1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Amirka suna fita Afganistan

Abdul-raheem Hassan
May 1, 2021

A hukumance dakarun Amirka 3,500 da sojojin NATO 7,000 sun fara ficewa daga kasar Afganistan, matakin da ke nuna alamar kawo karshen yakin sari ka noke na tsawon shekaru 20 a kasar.

https://p.dw.com/p/3spEX
Afghanistan Bundeswehr-Soldaten im Camp Pamir in Kunduz
Hoto: Tim Röhn/Imago Images

Wasu bayanai na nuna cewa gwamnatin Amirka ta kashe kudi sama da dala tiriliyon biyu kan sojojinta da ke Afganistan, tun bayan da suka mamaye kasar a shekarar 2001 bayan aukuwar harin ta'addanci na ranar 9 ga watan satumba a Amirka.

Sai dai janye sojojin na zuwa ne a dai-dai lokacin da adadin mutanen da suka mutu a sabon harin bam a masaukin baki da ke gabashin kasar ya karu zuwa 21, wasu 90 sun jikkata. Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin ko kuma harin yana da alaka da fara ficewar sojojin Amirka daga kasar.