1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta kashe sojojin Rasha 498

Suleiman Babayo ZMA
March 2, 2022

Mahukuntan Rasha sun tabbatar da cewa sojojinta kasar 498 suka halaka tun bayan kaddamar da kutse a kan Ukraine bisa umurnin Shugaba Vladimir Putin na Rasha.

https://p.dw.com/p/47ugD
Ukraine Krieg l Militärlastwagen mit einem schweren Artilleriegeschütz vom Typ 2S7 Pion bei Belgorod
Hoto: Mikhail Voskresenskiy/Sputnik/dpa/picture alliance

Mahukuntan Rasha sun tabbatar da cewa sojojin kasar 498 suka halaka sakamakon kutsen da suka kaddamar a kan Ukraine, kuma wannan shi ne karo ana farko da kasar ta fitar da alkaluman tun lokacin da Shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha ya ba da umurnin kutsen a makon jiya.

A cikin wata sanarwa da ya karanta Igor Konashenkov mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar ya ce sojojin Rasha kusan 500 sun gamu da ajalinsu, yayin da wasu 1,597 suka jikata sakamakon fafatawa da suke ci gaba da yi a kasar Ukraine mai makwabtaka.