1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea Conakry

September 5, 2021

Sojojin kasar Guinea Conakry, sun ayyana kifar da gwamnati tare da kama Shugaba Alpha Conde

https://p.dw.com/p/3zwo6
Videostill | Guinea Conakry - Militärputsch: Doumbouya hält Ansprache
Hoto: AFP

Wani faifan bidiyo ya nuna Laftanal Kanal Doumbouya, Zagaye da wasu sojojin, na cewa sun yanke shawarar jingine kundin tsarin mulki tare da tabbatar da kame shugaban kasar.

"Yace mun jingine kundin tsarin mulki, za mu dakatar da ayyukan hukumomin gwamnati sannan za mu rusa majalisar zartarwar gwamnati. Tare da hadin gwiwar dukkanin dakaru, za mu samo hanyar warware matsalolin da suka yi wa kasar nan dabaibayi."

Guinea Conakry | Videostill von mutmaßlicher Festnahme von Guineas Präsident Alpha Conde durch Militäreinheiten
Alpha Conde hambararren shugaban Guinea ConakryHoto: AFP

Su dai sojojin da suka sanar da kame shugaba Alpha Conde, sun ce tuni suka rufe iyakokin kasar na sama da kuma na kasa, baya ga dakatar da harkokin gwamnati.

Kasar ta Guinea da ke cikin jerin kasashe matalauta na duniya, wadda kuma ke alfahari da dumbin albarkatun karkashin kasa, ta kwashe shekaru tana fama da rashin daidaiton siyasa.