Sojoji sun sake kashe fara hula a Siriya
November 4, 2011Jamian tsaro a ƙasar Siriya sun kashe faran Hula guda 20 a garin Homs waɗanda suka buɗema wuta da bindigogi sa'ilin wata zanga zanga yayin da suka cfake wasu gomai a tsakiyar ƙasar.Wannan al'amari dai ya faru ne du kuwa da amince war da gwamnatin Bashar Al Assad ta yi da tayin ƙungiyar ƙasashen larabawa a taron ƙungiyar da ya gudana a ranar larba domin samun mafuta a rikicin siyasar da ya ƙiya ki canye wa.
Wanda gwamnatin ta Siriya ta amince ta janye sojojin ta daga cikin garuruwaN tare da sako yan adawar da ake tsare da su;tare da bada dama ga masu saka ido na ƙasashen duniya da kuma yan jaridu shiga ƙasar kafin soma tattauna ta neman sulhu tsakanin gwamnatin ta Siriya da yan adawar.ƙungiyoyin adawar dai ta hanyar shafin facebook sun yi kira ga magoya bayan su domin sake fitowa akan titunan a don gudanar da zanga zanga bayan sallah juma'a.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu