1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji na yin bore a Papua New Guinea

January 26, 2012

Sojojin na buƙatar shugaban ƙasar ya mayar da tsohon fFaministan ƙasar Michael Somare da aka sauke a shekara ta 2011 akan matsayin sa

https://p.dw.com/p/13pxK
Papua-Neuguinea Flagge
Tutar Papua New Guinea

Ratotannin daga Papua New Guinea na cewar wani habsan soja ya tabatar da karɓe ragamar rundunar sojojin ƙasar ;tare da jingine majalisar dokokin da kuma mayar da tsohon fraministan da aka sauke daga mulki Michael Somare a matsayin sa.

Habsan kanal Yaura Sasa mai ritaya wanda ya yi iƙirararin kan sa a matsayin shugaban askarawan ƙasar a Port Moresby babban birnin ƙasar ,a wani taron manema labarai da yayi ,ya ce ba juyin mulki ba ne ya yi, amma ya na buƙatar shugaban ƙassar Peter o -Neil ;ya sake mayar da fraministan akan aikin sa ,ya ce idan kuma bai yi haka ba ;to kam zai ɗau matakan da suka cancanta domin ceton dimokaradiyya.Tsohon fraministan Michael Somare mai shekaru 75 da haifuwa an sauke shi ne daga matsayin a tsakiyar shekara bara a lokacin da ya kai wata ziyara a Singapur domin yin jiya.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu