1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sami sojoji da laifin kashe abokan aikinsu

Ramatu Garba Baba
November 18, 2018

A garin Bambari na Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, sojoji uku ne suka mutu a yayin wata musayar wuta da ta auku a tsakanin rundunar sojoji biyu da aka tsugunar don kiyaye zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/38TSO
Bangui Zentralafrikanische Republik MINUSCA 09.10.2014
Hoto: picture-alliance/AA/Cyriaque Serefio

Akwai wasu da suka sami rauni a artabun da ya biyo bayan sabanin da aka samu a tsakanin bangarorin biyu.Tun bayan da rikicin kasar ya kazance, aka kuma tsugunar da rundunar wanzar da zaman lafiya, ake yawan samun barkewar fada inda sojojin ke kashe juna.

Majalisar Dinkin Duniya na da akalla jami'an wanzar da zaman lafiya dubu goma sha biyu da ta tura Afirka ta Tsakiya.

A makon da ya gabata majalisar ta amince da ci gaba da barin sojojin duk da sukan da ake musu na nuna gazawa a aikin tabbatar da tsaro.

An kwashi sama da shekaru shida ana fama da tashe-tashen hankula da ya tilastawa mutum sama da miliyan hudu rasa matsuguni.