1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na neman juya wa Faransa baya a fannin tsaro

Salissou Boukari MAB
August 4, 2023

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kalubalanci yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Faransa musamman ma fannin da ya shafi kasancewar dakaru da kuma matsayin sojojin da ke yaki da ayyukan ta’addanci a Nijar.

https://p.dw.com/p/4UnKS
Sojojin Faransa sun ta hada gwiwa da na Afirka don tabbatar da zaman lafiyaHoto: Getty Images/AFP/D. Benoit

Hukumar mulkin sojan Nijar ta CNSP ta ce mugayen halaye da kasar Faransa ke nunawa game da halin juyin mulki da ake ciki a kasar ne ya sa ta daukar matakin kalubalentar yarjejeniyar hulda tsakanin kasashen biyu a fannin tsaro. A yayin da yake magana kan wannan batu Mamane Sani Adamou da ke sharhi kan harkokin siyasa, ya danganta yarjejeniyar da aka sa hannu a kanta tun lokacin mulkin mallaka da abu mai kama da sakin talala. 

Niger | General Tchiani übernimmt Macht nach Putsch gegen Präsident Bazoum
Janar Tchiani ya nuna rashin amincewa da yarjejeniyar tsaron Nijar da FaransaHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Sani ya ce: "Yarjejeniyar ta tsaro ta ce duk wani arzikin karkashin kasa na Nijar za a sa shi a cikin gidauniya ta tsaro. Misali karfen uranium da man fertur da sauransu duk cikin tsaro suke, kuma yarjejeniyar ta ce idan Nijar ba za ta iya fitar da ma’adinan ba, dole Faransa za ta fitar, kuma sai ta ce ba ta so ne za a bai wa wata kasa . Wannan a rubuce yake duka, kuma irin wannan yarjejeniyoyi akwai su da dama tsakanin Nijar da Faransa."

Me zai faru bayan kalubalantar yarjejeniyar?

Niger - Macrons Truppenbesuch
Shugaba Macron na Faransa ya taba tattaunawa da sojojin kasarsa da ke NijarHoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Masu fafutikar kishin Afirka da sauran kungiyoyi masu neman ganin an shunfuda mulki na gaskiya da adalci sun ta yin kiraye-kiraye ga kasar ta Faransa da ta kwashe nata-ya-nata ta bar kasar Nijar Kamar yadda aka gani a  Mali da Burkina Faso. To me zai biyo bayan kalubalantar wannan yarjejeniya da sojoji suka yi? Mamane Sani Adamou ya ce:" Wannan yana daga cikin damar da wadannan sojoji da suka yi juyin mulki suka samu na cewa kafin a yi wani abu, sai an kalubalanci wannan yarjejeniya ta tsaro tsakanin Nijar da Farannsa. Domin akwai wata yarjejeniya ta 1961, akwai kuma sabbin yarjejeniyoyi da suka bada damar girka rundunonin soja wanda kowa bai san yadda aka yi su ba. Yanzu da aka yi haka dama ce ta a ce musu ku kwashe kayanku ku tafi."

Faransa na da sojoji kimanin 1500 da ta jibge a kasar Nijar. Amma sakamakon yanayin da ake ciki, ta kwashe 'yan kasarta kusan 600 daga kasar ta Nijar kwanaki kalilan bayan juyin mulki.