1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Ethiopiya sun kutsa cikin Somaliya domin daƙile al-Shabab

November 20, 2011

Ethiopiya ta bi sahun ƙasar Kenya wajen ƙoƙarin kawo ƙarshen ƙungiyar mayaƙan al-Shabab dake adawa da gwamnatin wucin gadin Somaliya

https://p.dw.com/p/13E1Z
Wasu daga cikin mayaƙan sa-kai a SomaliyaHoto: AP

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar wani jerin gwanon motocin dake ɗauke da sojojin ƙasar Ethiopiya sun kutsa cikin Somaliya ta hanyar garin Guriel, a wani abinda ake ganin buɗe sabon babi ne a ƙoƙarin yin fito na fito da mayaƙa ƙungiyar al-Shabab wadda ake dangantawa da ƙungiyar alQaeda. Kutsen dai na zaman wani yunƙuri mafi girman da dakarun ƙasar Ethiopiya ke yi zuwa Somaliya, tun bayan wata mamayar da suka ƙaddamar a shekarun baya, wadda kuma ta fuskanci turjiya daga 'yan ƙasar.

A cewar Sheikh Abdella Abdi dake goyon bayan gwamnatin wucin gadin Somaliyar dake tangal tangal, wadda kuma ke samun tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya, a wannan Lahadin ce sojojin na Ethiopiya suka haɗe da mayaƙan sa kai daya ke jagoranta, kana daga baya suka garzaya zuwa wani sansanin soji dake ƙudancin garin na Guriel. Abdi dai mabiyin ɗariƙar Sunni ne dake goyon bayan gwamnatin wucin gadin ƙasar ta Somaliya, wadda ke da rauni sosai. Sai dai kuma ya zuwa yanzu jami'an gwamnatin Ethiopia sun yi watsi da rahotannin dake cewar sun kutsa cikin Somaliyar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu