1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Burkina Faso: An kashe gwamman 'yan ta'adda

Abdoulaye Mamane Amadou LMJ
November 9, 2021

A Burkina Faso wani artabu da sojinin kasar suka yi da 'yan ta'adda ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan jihadi 15 a lardin Komadjari a yayin dakile wani mummunan harin da suka kudiri anniyar kaiwa.

https://p.dw.com/p/42kv5
Burkina Faso Symbolbild Anschlag
Hoto: Sia Kambou/AFP

Ma'aikatar tsaron kasar Burkina Faso ta ce wani sojanta daya ya rasu a yayin batakashin tare da kuma raunata wasu uku. Sai dai ko ba'idinsa rundunar tsaron ta Burkina Faso ta ce ta yi nasarar kwace muggan makamai a hannun mayakan ciki har da baburan da suke kai wa dakarun tsaron kasar hari da su.

Tun a shekarar 2015 ne dai kasar mai makwaftaka da Mali da Jamhuriyar Nijar ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga masu tsananin kishin addini, inda rahotanni suka ce an halaka fiye da mutum dubu biyu, wasu fiye da miliyan daya suka kauracewa gidajensu don tsira da ransu.