1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan kiyaye zaman lafiya ya mutu a Darfur

Halimatu AbbasApril 20, 2013

Yan bindiga sun halaka sojan kiyaye zaman lafiya a lardin Darfur na kasar Sudan da rikici ya yi wa kaka gida

https://p.dw.com/p/18Jtf
Hoto: Reuters

Wasu 'yan bindiga da ba a tantance ba sun hallaka daya daga cikin dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya a gabashin Lardin Darfur na Yammacin kasar Sudan, inda ake samun tashe-tashen hankula.

Kakakin dakarun ya tabbatar da haka, kuma wannan ya kawo yawan dakaru 44 da suka gamu da ajalinsu, tun cikin shekara ta 2007, lokacin da aka tura dakarun na kiyaye zaman lafiya.

Harkokin tsaro sun sukurkuce a Lardin na Darfur tun cikin shekara ta 2003 lokacin da kungiyoyin 'yan tawaye suka dauki makamai, domin gwagwarmaya da gwamnati da ke da mazauni a birnin Khartoum, saboda nuna wariya da suka ce suna fuskanta. Duk da tura dakarun kiyayen zaman lafiyan ana ci gaba da samun tashin hankali.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas