Sojan gwamnatin Siriya na kai farmaki
March 24, 2012Dakarun gwamnatin Siriya sun yini a yau suna kai farmaki kan inda yan tawaye suka fi ƙarfi. Shaidu sukace, sunga tankokin yaƙi soji suna tacilla rokoki a yammacin ƙasar.
Sabin alkalluman MDD, sun ce akalla mutane dubu 100 ne na kasar Siriya suka shiga halin gudun hijira a kasashe makwabta, musamman a ƙasar Turkiyya da Jordan sakamakon bata kashin da ake tsakanin dakarun gwamnatin Bashar Al-Assad da 'yan taway,e, wanda ya zuwa yanzu yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 10 daga bangarorin biyu. A nasu gefe kasashen duniya na cigaba da matsa kaimi ga shugaba Bashar-Al Assad, wanda ke da goyan bayan Rasha da China. A taron da suka shirya jiya birnin Brussels, ministocin harakokin wajen na kashen kungiyar tarayya Turai, sun kara tsuke takunkumi ga kasar Siriya.Ya zuwa yanzu mutane 126 ne, da suka hada da Bashar Al-Assad na na hannun damarsa aka haramtawa shiga kasashen Turai, sannan kuma aka saka takunkumi ga kudaden da suka mallaka a cikin bankunan kasahen EU. A safiyar yau tsofan sakarae Janar na MDD Kofi Annan da Majalisar ta dorawa yaunin shiga tsakanin rikicin Siriya, ya sauka a birnin Mosko na kasar Rasha, domin ganawa da hukumomin kasar game da batun.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdullahi Tank Bala