1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka da sojojin da ke mulki a Guinea

March 9, 2023

Hambararen Shugaba Alpha Conde na Guinea wanda ke zaune a Turkiyya inda aka ba shi mafakar siyasa na ci gaba da furta kalamai da ke daukar hankulan 'yan kasarsa.

https://p.dw.com/p/4OSNy
Tsohon Shugaba Alpha Condé na Guinea
Tsohon Shugaba Alpha Conde na GuineaHoto: Thierry Gouegnon/REUTERS

Hambararen shugaban kasar Guinea Conakry Alpha Conde wanda ke zaune a Turkiyya inda aka ba shi mafakar siyasa na ci gaba da furta kalamai da ke daukar hankulan 'yan kasarsa. Ko da a baya-bayan nan a yayin wata hira da aka yi da shi, Conde ya ce ya kira magoya bayan jam'iyyarsa ta RPG da su yunkura domin karbe mulkin daga hannun sojojin kasar.

''Ku kasance cikin shirin ko ta-kwana, ku aike mun da lambobin shugabannin kungiyoyin matasa da na mata'' wannan su ne kalaman farko da Alpha Conde ya furta a yayin hirar sa da wata kafar sardarwa ta kasar Guinea tun bayan da sojoji karkashin kanal Mamady Doumbouya suka kifar da gwamnatinsa a shekarar 2021. Mognouga Cisse dan jaridar da ya yi hira da hambararen shugaban ta wayar tarho ya ce Alpha Conde na son ya yi ramuwar gayya ga sojojin da suka yi masa juyin mulki.

Karin Bayani: Guinea: Shekara guda da kifar da gwamnati

Guinea I Mamady Doumbouya
Kanar Mamady Doumbouya- shugaban gwamnatin mulkin sojan GuineaHoto: Xinhua/imago images

Babban abin da ya fi bakanta wa Alpha Conde rai shi ne na ganin makusantasa ne suka kitsa masa juyin mulkin na ranar 5 ga watan Satumban 2021, wannan ne ma ya sa Conde ya mika tayi ga babban abokin hamayarsa Cellou Dalein Dialo don kawai ya cika burinsa.

To sai dai ga Ibrahim Teneba Kourouma shugaban wata jam'iyya a Guinee, na ganin tsohon shugaban na babatu a kafafen sadarwa ne kawai domin share wa jam'iyyarsa ta RPG hanya yayin da ake tunkarar zaben kasar da ke tafe a shekarar 2024.

To sai dai ga mai sharhi kan harkokin siyasa Kabinet Fofana, ya ce tsohon shugaba Conde na nema ne kawai ya sake farfado da kimarsa a fagen siyasar kasar bayan ya share wa'adi 2 a kan gadon mulki.

Hambararen shugaban dai ya kafa wata hadaka tare da manyan jam'iyyun kasar cikin har da UFGG ta babban abokin hamayarsa Cellou Dalei Diallo, da kuma UFR ta Sidya Toure da kuma Front National pour la defense de la Constitution. A kiraye-kirayen da jam'iyyun kasar suka yi na a fito a yi zanga-zanga a wannan Alhamis, ba a bar shi a baya ba duk da yake sojojin da ke mulki sun soke gangamin don gudun sake samun tashen-tashen hakali a kasar.

Daga gidansa na Turkiyya inda ya samu mafakar siyasa tsohon shugaban na Guinea na ci gaba da kiran magoya baya da shirya yin gwagwarmar dawo da kasar kan tafarkin dimukuradiyya, inda ya tura masu sakon cewa ya yaga wasikar marabus da ya yi daga gadon mulki da sojoji suka tilasta masa ya rubuta a washe garin harbarar da gwamnatinsa.