Siyasar Chadi: Deby ya kaddamar da yakin neman zabe
April 15, 2024Gwamnatin Mahamat Deby na daga cikin mulkin da sojoji suka kafa da ya ja hankalin kasashen duniya, wanda kuma ya gurgunta tsarin dimukradiyya a kasar da ke yammacin Afrika.
Karin bayani: Chadi: An hana wasu 'yan adawa takarar shugaban kasa
Chadi ce kasa ta farko da ta shirya gudanar da zabe daga cikin kasashen da sojoji ke mulki nahiyar Afrika, duk da kiraye-kirayen kasashen duniya na mika mulki ga farar hula, a zaben da aka shirya gudanarwa a watan Mayun 2024.
Karin bayani: Kotu ta tantance masu tsayawa takara a kasar Chadi
A yayin da yake jawabi ga dandazon magoya baya a birnin N'Djamena, Deby ya jaddada cewa za a gudanar da zabe domin dawo da kasar kan tafarkin dimukradiyya tare da tabbatar da cewa zai cika alkawari wajen dora kasar kan gwadabe mai kyau kasancewar sojoji na martaba alkawari musamman batun tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki.