1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar ƙasar Girka na tangal-tangal

May 16, 2012

'Yan siyasan Gikra sun kasa warware bance-bancen dake tsakaninsu don haka sai an sake shirya zaɓe

https://p.dw.com/p/14wEq
From left to right, leader of the Democratic Left party Fotis Kouvelis, head of the Socialist PASOK party Evangelos Venizelos, leader of Conservatives New Democracy party Antonis Samaras, Greek President Karolos Papoulias, leader of the Coalition of the Radical Left party Alexis Tsipras and leader of the 'Independent Greeks', Panos Kammenos pose during a Political party leaders meeting at the Presidential Palace in Athens, on Tuesday, May 15, 2012. Greec's president met the leaders of five political parties, broadening talks to try and form a coalition government and end a nine-day deadlock in the crisis-hit country. (Foto:Aris Messinis, pool/AP/dapd)
Hoto: dapd

Shugabannin siyasa a ƙasar Girka sun haƙura da batun kafa gwamnati, bayan jerin tattaunawa da aka yi tsakanin manyan jam'iyun ƙasar, amma aka kasa kafa gwamnati tun bayan zaben da ya gudana kwanaki tara. Hakan dai yana nufin ba makawa za a gudanar da zabe a tsakiyan watan gobe. A yaune ake saran shugaban ƙasar ta Girka zai sanar da ranar yin zaben, kana ya nada gwamnatin wucin gadi. Abinda ya hana akafa gwamnati dai shine banbancin ra'ayi kan bashin EU da asusun IMF na Euro biliyan 130 da aka baiwa ƙasar don ceto tattalin arzikinta. Rikicin siyasan ƙasar ta Girka dai zai iya sa ƙasar ta pice daga cikin ƙasashe masu amfani da kudin Euro. Zaɓen da ya gudana a farkon watan nan ya gaza fidda dan takaran da ya yi nasara tsakanin jam'iyyun da ke goyon bayan shirin tsuke bakin aljihu da masu adawa da tsarin.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu