1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya za ta fiskanci tsauraren takunkumi

August 24, 2011

Ƙasashen yamma sun tsara jerin takunkumin da suke buƙatar a azawa shugaban ƙasar Siriya Bashar al-Assad da muƙarrabansa

https://p.dw.com/p/12NCj
Shugaban Siriya Bashar al-AssadHoto: dapd

Ƙasashen Jamus, Faransa, Birtaniya da Portugal sun tsara daftarin sakawa shugaban Siriya Bashar Al-assad da muƙarrabensa takunkumi, domin ladabtar da ita bisa yadda gwamnati ta kai farmaki kan fararen hula da suka yi mata bore. Ƙudurin wanda ke matuƙar samun goyon bayan Amirka, zai shafi aƙalla muƙarraben shugaban 23. Kana ƙudurin ya kumshi takunkumin hana sayarwa Siriya makamai. An dai rabawa wakilan kwamitin sulhu na MDD takardun wannan ƙudurin. MDD ta ƙyasta cewa aƙalla mutane 2,200 suka mutu a farmakin da dakarun Siriya suka kaiwa waɗanda suka yi boren kifar da gwamnati, a tsawon watanni biyar da suka gabata.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasir Awal