'Yan tawayen Siriya za su mika garuruwansu
June 29, 2018Rahotanni daga kasar Siriya na cewa gwamnatin Bashar al-Assad da wakillan 'yan tawaye sun soma tattaunawa a wannan Juma'a kan batun mika wa gwamnatin garuruwan Kudancin kasar ta Siriya da ke a hannun 'yan tawayen da nufin kauce wa fuskantar farmakin da sojojin gwamnati suka kaddamar da nufin kwato yankin.
A ranar 19 ga wannan wata na Yuni ne sojojin gwamnatin Siriya masu samun dafawar sojojin Rasha suka kaddamar da farmaki ta kasa da kuma ta sama a jihar Daraa da ke a hannun 'yan tawaye da kuma ake yi wa kallon tushen bijirewar da aka soma yi wa gwamnatin Al-Assad a shekara ta 2011.
Da ma dai a kwanaki biyu da suka gabata 'yan tawayen sun mika wa sojojin gwamnatin Siriyar wasu garuruwa uku na jihar ta Deraa a cikin laluma inda su kuma mayakan tawayen aka ba su damar ficewa daga cikin garuruwan inda suka bar tarin manyan makaman da suka mallaka.