Siriya ta ƙaryata batun murabus na muƙaddashin shugaban ƙasa
August 18, 2012Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Siriya ta karyata jitan-jitan da a ke ta bazawa na murabus din mukadashin shugaba Bashar Al-Assad.
A jiya Juma'a ne wasun kafofin yada labaran yammaci suka bayana cewar Farouk al-Chareh ya canza sheka inda ya samu mafuka a kasar Jodan. Gidan talabijan mallakar gwamnatin ta nuna hotunan mukadashin tare da shugaban kasa Asad a zaman taron majalissar ministocin jiya Juma'a. Hasali ma gidan talabijan din ya karanto wata sanarwa daga mukadashin inda ya ke goyon bayan nadin da a kawa Lakhdar Brahimi manzo na musamman a rikicin kasar ta Siriya. To saidai a wani labarin kuma dakarun gwamnati na ci-gaba da kan hare-hare ba kaukkautawa ga masu yunkurin kifar da gwamnatin inda kusan mutane 35 a ke hallaka a yankunan Allepo da kuma Azzaz.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi