1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta zargi Isra'ila da kai mata hari

March 22, 2023

Hukumomi a Siriya na cewa a karo na biyu cikin wata guda, Isra'ila ta sake kai hari ta sama a safiyar wannan Larabar a filin jirgin sama na Aleppo da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4P2om
Masu yakar gwamnatin SiriyaHoto: Salah Al-Ashkar/AFP/Getty Images

Kafofin yada labarai ba su ruwaito samun asarar rayuka a harin ko wasu da suka jikkata ba. Rahotanni sun yi nuni da cewa jiragen yakin Isra'ila sun harba makamai masu linzami zuwa birnin da ke zama mafi girma a Siriya.

Filin jirgin sama na Aleppo na daga cikin manyan hanyoyin da ake jigilar kayan agaji zuwa kasar Siriya tun bayan aukuwar iftila'in girgizar kasa a watan Fabarairun da ya gabata. Ko a ranar 7 watan Maris din nan da muke ciki, harin da Isra'ilar ta kai ya yi sanadiyar dakatar da ayyukan tashi da saukan jirage na tsawon kwanaki kafin kammala gyaran asarar da harin ya haifar.