1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta yi watsi da sabon mai shiga tsakani

August 20, 2012

Kalaman sabon mai shiga tsakanin rikicin kasar Siriya Brahimi sun janyo takaddama.

https://p.dw.com/p/15tM6
Diplomat Lakhdar Brahimi speaks with former U.S. President Jimmy Carter (not pictured) during a joint news conference in Khartoum in this May 27, 2012 file photo. Veteran Algerian diplomat Brahimi is expected to be named to replace Kofi Annan as the U.N.-Arab League joint special envoy for Syria barring a last-minute change, diplomats said on August 10, 2012. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah/Files (SUDAN - Tags: POLITICS)
Lakhdar BrahimiHoto: Reuters

Ƙasar Siriya ta yi watsi da naɗin Lakhdar Brahimi a matsayin mai shiga tsakanin kan rikicin ƙasar, saboda da kalaman da ya yi cewa halin da ake ciki ya zama yaƙin basasa, wanda saidai a nemi shawo kansa.

Brahimi jami'in diplomasiyar ƙasar Algeriya, shi ne ya karɓi Kofi Annan, kan shiga tsakanin magance rikicin na ƙungiyar kasashen Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya.

An kuma ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a birnin Aleppo. Sannan rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 52 da suka haɗa da yara sun hallaka a garin Deraa. Haka na zuwa bayan ƙarewar wa'adin jami'an saka ido na MDD da aka tura ƙasar ta Siriya.

A wani labarin, Shugaban Faransa Francois Hollade, yayin ganawa da mai shiga tsakanin Brahimi, ya ce kawar da Shugaba Assad na Siriya shi ne kawai zai samar mafita kan rikicin ƙasar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu