Siriya ta tsunduma cikin yaki: inji Assad
June 27, 2012Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya ayyana cewa kasarsa na cikin yaki tsundum bayan watanni 15 tana fama da rigingimu na cikin gida. Da yake jawabi wajen rantsar da sabbin yan majalisar gudanarwar gwamnatinsa a jiya, shugaba Assad ya ce gwamnati za ta yi amfani da dukkan matakan da suka dace wajen samun nasara a wannan tarzoma.
" Yace Syria ta sami kanta a cikin yaki, a saboda haka idan mutum ya kasance a cikin yanayi na yaki, to kuwa zai iya yin amfani da matakan da suka dace ta kowace hanya domin samun nasara".
A can makobciyarta kasar Turkiya Firaminista Racep Tayyip Erdogan ya yi barazanar daukar matakin soji akan Damascus matukar sojojin Syria suka kusanci kan iyakar Turkiya. Gargadin ya zo ne bayan harbo jirgin Turkiyan da Syria ta yi a makon da ya gabata.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu