1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar ƙyale masu sa ido na Larabawa shiga ƙasar

December 19, 2011

Ministan harkokin wajen Siriya Faisal al-Makdad ya sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Alƙahira hedkwakar ƙungiyar ƙasashen Larabawa.

https://p.dw.com/p/13VYn
FILE - A pro-Syrian regime protester waves a Syrian flag as he stands in front of portrait of Syrian President Bashar Assad, during a protest against sanctions, Damascus, Syria, in this Dec. 2, 2011 file photo. Speaking to ABC's Barbara Walters in a rare interview that aired Wednesday, Dec. 7, 2011 President Bashar Assad maintained he did not give a command "to kill or be brutal." (AP Photo/Muzaffar Salman, File)
Hoto: dapd

Watanni tara bayan fara boren ƙin jinin gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad, ƙasar Siriya ta ba wa masu sa ido na ƙasa da ƙasa izinin shiga ƙasar. Mataimakin ministan harkokin wajen Siriya Faisal al-Makdad ya sanya hannu kan yarjejeniyar aikewa da tawagar masu sa ido na ƙasashen Larabawa ƙasar. Tun a cikin watan Nuwamba a hukumance gwamnatin birnin Damaskus ta amince da wani shirin ƙasashen Larabawa na kawo ƙarshen mummunan rikicin, amma ta ci-gaba da ɗaukar matakan ba sani ba sabo kan masu zanga-zangar ƙyamar gwamnati. Tawagar jami'an sa idon za ta tabbatar da an yi aiki da ƙa'idojin yarjejeniyar. Bisa ƙiyasin Majalisar Ɗinkin Duniya mutane fiye da 5000 aka kashe tun bayan fara boren ƙin Assad a cikin watan Maris. A kuma halin da ake ciki Faransa ta yi kira da a gaggauta aikewa da tawagar sa idon zuwa Siriya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala